ABNA24 : A wata sanarwa da ma’aikatar Kwadago ta Nijeriyan ta fitar ɗauke da sanya hannun mataimakin daraktan Ma’aikatar Charles Akpan, tace ministan ƙwadago na Nijeriyan Chris Ngige ne ya kafa kwamitin.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriyan NAN ya ba da rahoton cewa kwamitin dai yana ƙarƙashin jagorancin babban sakataren Ma’aikatar ne Peter-Yemira Tarfa, waɗanda sakataren gwamnatin jihar Kadunan, Balarabe Lawal da kuma mataimakin shugaban Кungiyar kwadago ta ƙasar Najim Hashim za su taimaka masa.
Ministan ƙwadagon dai ya ce yana fatan ‘yan kwamitin za su yi ƙoƙari wajen magance rikicin da ya kunno kai tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da ƙungiyar ƙadagon, inda ya ba wa kwamitin kwanaki 21 da ya gama aikin nasa da kuma gabatar masa da rahoto.
Kafa kwamitin dai ya zo ne a ƙoƙarin da gwamnatin Nijeriyan take yi wajen dawo da lamurra daidai a jihar ta Kaduna musamman bayan korar ma’aikata masu yawa da gwamnatin jihar ta yi lamarin da ya haifar da zanga-zangogi da kuma yajin aiki a jihar.
342/